Gamayyar kungiyoyin matasa sun roki Uba Sani ya fito takarar Sanata na Kaduna ta Tsakiya

0

Kungiyoyin Matasa sun roki Uba Sani ya gaggauta amsa kiran mutanen jihar Kaduna ya fito takarar Sanatan Kaduna ta tsakiya.

Kungiyoyin matasan sun bayyana haka ne bayan kammala wani ganawa da suka yi da sauran mambobin kungiyoyin a Kaduna.

Shugaban gamayyar kungiyoyin Umar Mohammed, wanda ya shaida wa PREMIUM TIMES HAUSA a Kaduna cewa, “ Yin haka ne kawai ya dace wa mutanen Kaduna ta tsakiya.

“ Bayan jajircewa da yayi a harkar siyasa, Uba mutum ne da ya ke da kishin talakawa. Taimaka wa gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai kawai yake yi amma abubuwan da yake yi wa matasa kawai ya fi wadanda muka zaba ma.

“ Uba ya samarwa mutanen Kaduna aiyukan yi bayan makarantu da yake biya wa marayu da mata da suka rasa mazajen su.

Mun zazzagaya mun ga haka. Ni da kaina na tafi garuruwa da dama da kauyuka, zai yi wuya baka ji wani yana yabon Uba Sani ba.

“ Dalilin haka ne ya sa muka taru dukkan mu domin mu fito karara mu roke shi ya bayyana ra’ayin sa domin hankalin mu ya kwanta.

Umar Ya kara da cewa tabbas suna ganin fastocin sa, hakan bai kwantar musu da hankali ba haryan zu.

“ Mu dai burin mu muji ka amsa wannan kira, kuma za mu ci gaba da yi maka wannan kira akai-akai har sai ka fito kace za kayi.

Idan ba a manta ba wata kungiya mai suna ‘Kaduna Democracy Monitors’ ta ce ta tsaida Malam Uba Sani a matsayin wanda ya cancanci yin takarar kujerar sanatan Kaduna ta tsakiya a 2019.

A takarda ta musamman da kungiyar ta fitar bayan zaman ta, kakakin kungiyar Abdullahi Kwarbai ya bayyana cewa Uba Sani ya cancanci yabo musamman ganin yadda ya jajurce wajen nuna adawar sa ga mulkin soji a kasar nan a wancan lokacin da yayi sanadiyyar dole suka hakura da mulkin.

“ Irin halaye na Uba Sani da suka hada da girmama na gaba, yin siyasa ba da gaba ba da son jama’a ya sa muka ga babu wanda ya cancanci wannan kujera na sanata in ba shi ba a 2019.

Shugabannin jam’iyyar APC na kananan hukumomi shida cikin bakwai na Kaduna ta tsakiya suma a kwanankin baya sun amince masa ya fito ya tsaya takarar kujeran sanata na Kaduna ta tsakiya a 2019.

Har yanzu dai Uba Sani bai bayyana ra’ayin sa ko zai tasya takara ba , sai da ga dukkan alamu zai lokaci kawai ake jira..

Share.

game da Author