Majalisar dokokin jihar Kogi ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta yi wa makiyayan jihar rajista cewa hakan zai taimaka wajen samar da tsaro a jihar.
Majalisar ta tattauna haka ne a zauren majalisa ranar Laraba.
Shugaban masu rinjaye na majalisar Bello Abdullahi Balogun ne ya jagoranci mahawaran, sannan ya kara da cewa yin hakan zai taimaka wajen sanin yawan makiyayan da ke kiwo a jihar.
Abdullahi–Balogun ya yi kira ga gwamnati, kananan hukumomi da ma’aikatar kula da aiyukan kananan hukumomi da sarakunan gargajiya da su hada hannu don ganin an yi wa makiyaya a jihar rajista.
Sauran ‘yan majalisan da suka goyi bayan wannana kudiri sun hada da Hassan Abdullahi mai wakiltan Dekina II jam’iyyar APC, Ahmed Mohammed mai wakiltan Ankpa I jam’iyyar APC, Oluwatoyin Lawal mai wakiltan Yagba West jam’iyyan PDP.
Daga karshe kakakin majalisar Matthew Kolawole ya ce lalle yi wa makiyaya rajista zai taimaka wajen kama wadanda suke yin amfani da rikicin makiyaya da manoma suke aikata laifuka.
Discussion about this post