‘Yan kunar bakin wake sun ta da bam a sansanin ‘yan gudun hijira dake Dalori

0

Shugaban hukumar bada agajin gaggawa na jihar Barno SEMA Satomi Ahmed ya sanar da hari da wasu ‘yan kunar bakin wake biyu suka kai sansanin yan gudun hijra da ke Dalori.

Ahmed ya ce sandiyyar wannan hari mutane biyar sun rasa rayukan su sannan mutane 39 sun sami rauni.

Ya ce ‘yan kunar bakin waken da ya hada da mace da namiji sun kai wa sansanin Dalori hari ne da misalin karfe 8 na yamman Laraba.

” Mace ce kadai ta sami shiga cikin sansanin inda ita da mutane biyar suka mutu sannan wasu 39 suka sami rauni sanadiyyar bam din da ta tada amma shi namiji bai sami shiga sansanin ba saboda bam din dake rataye a jikin sa ya tashi kafin ya shiga cikin sansanin.”

Bayanai sun nuna cewa har yanzu jami’an tsaro basu ce komai ba game da wannan hari.

Share.

game da Author