Kungiyar ma’aikatan hukumar inshorar kiwon lafiya ta kasa NHIS sun gudanar da zanga-zanga yau Alhamis a ofishin hukumar da ke Utako, Abuja don nuna rashin jin dadin su da dawo da tsohon shugaban hukumar Usman Yusuf aiki.
Shugaban kungiyar Razaq Omomeji ya bayana cewa hakan da gwamnati ta yi bai yi musu dadi ba ko kadan.
” Muna kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya kara gudanar da bincike kan zargin da aka yi kan Yusuf kafin ya dawo da shi kan aiki saboda har yanzu akwai zaman kotu da yake fuskanta da ba a gama ba. Sannan da Buhari ya hakura tukuna hukumar EFCC ta kammala binciken da take yi kan Yusuf kafin ya dawo da shi.”
Buhari ya dawo da Usman Yusuf kan aikin sa ne ranar Talata bayan dakatar da shi daga da ministan Kiwon lafiya Isaac Adewole ya yi na tsawon watanni shida.
A dalilin rashin jituwa tsakanin minista da shugaban NHIS din, shugaba Buhari ya gaiyaci ministan mai rikon kujeran shugaban cin Attahiru Ibrahim domin su tattauna sannan su sulhunta tsakanin su da Usman Yusuf din.
Idan ba a manta ba, da yammacin Alhamis din 6 ga watan Yulin 2017 ne ministan lafiya Isaac Adewole ya dakatar da shugaban hukumar bada inshorar kiwon lafiya ta Kasa ‘NHIS’ Usman Yusuf daga aiki.
Ministan Kiwon Lafiya Isaac Adewole ne ya sanya hannu a takardar dakatarwar.
Ana tuhumar Usman Yusuf da yin amfani da wasu kudade da ya kai naira Miliya 200 don gudanar da tirenin ga wasu ma’aikatan hukumar da kuma rashin jituwa dake tsakanin sa da ministan kiwon lafiya Isaac Adewale.
Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya ce wasu daga cikin dalilan da ya sa ya dakatar da shugaban hukumar inshorar lafiya lafiya ta kasa NHIS Usman Yusuf shine don korafe-korafen da ake tayi kan sa na sama da fadi da yayi da wasu kudaden ma’aikatan da kuma zargi da akeyi masa na aikata wasu laifuka da ya saba wa dokar ma’aikatar.
Minista Isaac Adewole ya ce ya dakatar da Usman Yusuf na tsawon watanni uku ne saboda a sami damar gudanar da bincike akan zargin da akeyi a kansa.