Fulani basu kai wa matafiya hari a hanyar Legas ba – Rundunar ‘Yan sanda

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta karyata wata jita-jita da ake ta yadawa wai wasu makiyaya na kai wa matafiya a hanyar Legas zuwa Ibadan hari.

Rundunar ta ce wannan labarin gizo da koki ne kawai amma bashi da tushe ko kadan. Sannan ta sanar cewa wannan jita-jita ta samo asali ne a labaran karerayi da ake yada wa a yanar gizo.

Kakakin rundunar jihar Abimbola Oyeyemi ta ce da jin iri wadannan labarai sai suka hanzar ta kai samame hanyoyin inda suka gane cewa maganar babu gaskiya a cikinta.

Abimbola ta ce sun gano cewa jita-jita ne kawai wasu mutane ke yi don neman tada zaune tsaye ke.

Ta kuma yi kira ga mutane da su ci gaba da harkokin su sannan ta tabbatar da cewa rundunar na iya kokarin ta na ganin ta kama wadanda suka yada wannan jita-jita don hukunta su.

Share.

game da Author