Sankarau ta yi ajalin mutane uku a Yobe

0

Kwamishinan kiwon Lafiya na jihar Yobe Bello Kawuwa ya bayana cewa a bana mutane 10 sun kamu da cutar Sankarau kuma cutar ta yi ajalin mutane uku a jihar.

Kawuwa ya fadi haka ne a Damaturu ranar Laraba da yake kaddamar da fara yin allurar rigakafin cutar.

Ya kuma kara da cewa bana dai gwamnati, hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko da kungiyoyin bada tallafi sun hada hannu domin fara yin rigakafin cutar ta wuri.

Ya ce za su yi wa yara ‘yan shekara daya zuwa shida allurar rigakafin cutar da suka kai 771,778 a duk kananan hukumomin jihar daga ranar 7 zuwa 18 ga watan Fabrairu.

Daga karshe Kawuwa ya yi kira ga iyaye da ma’aikatn kiwon lafiya da su tabbata an yi wa ‘ya’yan su wannan allura.

Share.

game da Author