Ban san da shirin kara farashin fetur ba – Kachikwu

0

Manyan jami’an gwamnatin tarayya biyu sun yi sabani dangane da batun yiwuwar karin kudin man fetur.

Gwamnan jihar Bauchi Mohammed Abubakar ya bayyana cewa, biyo bayan taron da gwamnoni su ka yi da Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, ya nada gwamnan jihar Gombe Ibrahim Dankwambo, ya shugabanci kwamitin da zai zauna tare da jami’an NNPC su tantance farashin mai, bisa yin la’akari da yadda ake sayar da shi a kasashen da ke makwabtaka da Najeriya.

Sai dai kuma Karamin Ministan Fetur, Ibe Kachikwu, shi kuma ya ce bai san da wani shiri na kara farashin fetur ba.

Yayin da gwamnati ke ta hakilon musanta yunkurin kara farashin mai, shi kuma gwamnan jihar Bauchi ya ce tuni an kafa kwamiti, domin a zaman su da gwamnonin da Osinbajo, an tattuana cewa babban dalilin da ya sa fetur ke matsanancin karanci a kasar nan, shi ne sumogal din sa da dillalan fetur din ke yi zuwa kasashe makwabta da Najeriya domin su rika sayarwa da tsada.

A kan haka ne gwamnan ya ce kwamitin su zai duba farashin litar fetur a kowace kasar da ke makwabtaka da Najeriya.

Yayin da ake sayar da lita daya naira 145 a Najeriya, abin lura shi ne karancin sa ya sa tilas ana saye a kan naira 200 a hannun ‘yan bumburutu.

Wani bincike kuma ya tabbatar da cewa a kasar Chadi naira 350 ake sayar da lita daya.

Yayin da NNPC ke dora alhakin matsalar fetur kan masu yin fasakwaurin sa, su kuma masu sukar yanayin mulkin APC na dora laifin kacokan kan gwamnatin tarayya saboda ta kasa hana a rika yin fasakwaurin fetur din.

Shugaban NNPC, Maikanti Baru, ya kara dora laifin a kan dan karen tsadar da kudaden kasashen waje suka yi, inda ake canja naira sama da naira 360.

“A yanzu fa babu wani kamfanin saida mai na masu zaman kansu da ke fita waje ya na sayo fetur. NNPC ce kadai ke sayo tataccen mai daga kasashen waje. Ita ma din ta na jin jiki sosai, domin kudin dakon sa ya karu sosai da sosai.”

Yanzu dai ana cikin tsaka-mai-wuya ce. a gefe daya ga wahalar fetur, ga dogayen layukan shan mai, ga kuma tsadar da ake sayen fetur din a hannun ‘yan bumburutu, sannan kuma gwamnati ta ce kudin saukalen fetur daga kasashen waje ya karu.

Gwamnati ta ce idan ta sayo litar fetur daga waje, to har ya na kamawa naira 171.

Share.

game da Author