INEC ta kafa kwamitin da zai binciki zaben Kananan Hukumomin Kano

0

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, bayyana cewa ta kafa kwamitin da zai bincikin yadda aka yi kananan yara suka rika dangwala kuri’u a zaben kananan hukumomin jihar Kano.

An dai rika nuno yadda kananan yara suka daddangwala kuri’a ba ji ba gani a lokacin zaben.

Ganin yadda jama’a a fadin kasar nan su ka rika yin Allah-wadai da zaben, INEC ta fito ta nesanta kan ta da zaben, ta na nuni da cewa hukumar zaben jihar Kano ce ta shirya zaben, kuma dama ita ce ke da alhakin shirya zaben kananan hukumomi a jihar ta.

Shugaban INEC na kasa baki daya, Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa kwamitin zai fara aiki cikin sati mai zuwa. Ya yi wannan jawabi ne a wurin da ake gudanar da taron sanin-makamar-shirya-zabe da ke gudana yanzu a dakin taro na otal din Intercontinental, a Lagos.

Share.

game da Author