An kama wasu makiyaya da makamai a jihar Benuwai

0

Dakarun sojin Najeriya dake aiki kauyen Yelwata jihar Benuwai sun kama wasu makiyaya 10 suna barnata amfanin gona a wasu kauyuka dake yankin.

Wani dakare cikin su mai suna Texas Chukwu ne ya bayyana haka a Abuja.

Ya ce yayin da makiyayan suka hango dakarun na zuwa wajen su sai suka tsere cikin daji.

” Ko da suka ruga haka bai hana mu kamo su ba domin bin su muka yi har ciki dajin muka kamo su.”

Chukwu ya ce cikin abubuwan da suka kwato a hannun makiyayan sun hada da babura biyar,adduna biyu, layu da guraye da tsabar kudi har Naira 120,000.

Ya ce sun mika su ga hukumar ‘yan sanda domin ci gaba da gudanar da bincike a kan su.

Share.

game da Author