‘YAN MATAN #Dapchi: Sata ce ko Siyasa ce? Alamomin Tambaya 14 masu daure kai

0

Ba daliban makarantar kwana ta Sakandaren Koyon Kimiyya da Fasaha ta Dapchi da ke cikin Jihar Yobe ne Boko Haram su ka fara sacewa su yi garkuwa da su ba. An sace na makarantar Chibok cikin 2014, inda duk da cewa an karbo sama da 80, har yanzu akwai sama da 100 a hannun Boko Haram.

Boko Haram sun fara yunkurin satar daliban sakandare da nufin yin garkuwa da su, tun a cikin 2013, da su ka yi nufin sace daliban sakandaren maza da mata ta garin Bajoga da ke jihar Gombe.

A lokacin an yi gaggawar sanar da gwamnatin jihar halin da ake ciki cewa Boko Haram sun tunkari makarantar, inda nan da nan aka tattara daliban aka gudu da su a cikin jeji, daga nan aka shirya motoci tare da jami’an tsaro da yawa suka je suka kwaso su gaba daya, aka tsirar da su.

DALIBAN DAPCHI

1 – Abu na farko mai daure kai, shi ne yadda aka sace ‘yan matan a daidai lokacin da jami’an soja da fadar shugaban kasa ke ikirarin cewa an kakkabe Boko Haram, shi kansa Shekau ta sa ta kusa karewa, ya zama kyanwar Lami, bai iya cizo balle yakushi.

2 – An sace ‘yan matan a jihar Yobe, jihar da Hafsan Hafsoshin Askarawan Najeriya, Janar Tukur Buratai ya ke.

3 – An sace ‘yan matan kuma an yi doguwar tafiya sama kilomita 200 kafin a fice da su daga Yobe a keta Barno ko Jamhuriyar Nijar kamar yadda wasu kafafen yada labarai suka ruwaito.

4 – An sace su a daidai lokacin da hukumar tsaro ta sojoji ke jinjina wa kanta cewa ta fatattaki Boko Haram, duk sun tarwatse, an kashe na kashewa, an kama na kamawa, kuma babu su a cikin Sambisa, duk an suburbude su karkaf.

5 – An sace su a daidai lokacin da guguwar zaben 2019 ta danno gadan-gadan, kamar yadda aka sace na Chibok, a cikin 2014, a lokacin da guguwar zaben 2015 ta tirnike.

6 – An bayyana cewa an ceto akasarin wadanda aka sace din, daga baya kuma aka bayar da hakuri cewa ba a gano kowa ba.

7 – Yaya aka san wani bangaren Boko Haram ne na su Mamman Nur suka sace daliban, ba bangaren Shekau ba, kamar yadda wasu ruwayoyi suka nuna?

8 – An rika kutubal-bal da tunanin ‘yan Najeriya. Yayin da gwamnan Yobe ya ce sace daliban laifin janye sojoji ne daga Dapchi, su kuma sojoji na cewa ba a girke soja a Dapchi ba.

9 – Jamiyya mai mulki, APC da PDP sun rika sukar juna dangane da sace daliban.

10 – Gwamnatin Buhari ta rika yin dawurwura dangane da hakikanin abin da ke faruwa, daga baya ta tura tawagar tantancewa.

11 – Akwai daure kai a ce a loda dalibai sama da 100 a cikin motoci kamar yadda ake lodin shanu, kuma a gudu da su a yanayi na doguwar tafiya, a ce kuma ba a san inda su ke ba.

12 – Akwai daure kai sosai da kuma tunanin abin da zai rika biyo baya, gani da kuma jin cewa hukumar sojojin kasar nan sun ce ba su iya tabbatar da tsaro a ilahirin makarantun jihar Barno da Yobe. To me ke mafita ga daliban wadannan jihohi, musamman na karkara kamar Dapchi da sauran su?

13 – Tuni ake yi wa gwamnatin Buhari hannun-ka-mai-sanda cewa ta daina ikirarin cewa ta gama da Boko Haram, tunda a kullum su na ci gaba da fada da sojojin Najeriya. Amma gwamnati da sojoji na cewa sun gama da Boko Haram.

14 – Zai yi wuya wani jamai’in gwamnati ko hukumar sojoji su sake fitowa su ce sun gama da Boko Haram kuma a yarda da bayanin su. Ko sun fada ba mai yarda da su.

15 – … Sata ce ko siyasa ce ?

Share.

game da Author