Jakadan Najeriya da ke Chana, Wale Oloko, ya bayyana cewa da yawan ‘yan Najeriya na tsare a kurkuku daban-daban na kasar Chana, saboda sun wuce wa’adin zaman kasar da ke rubuce a biza din su.
Oloko ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) a Lagos cewa wasu ‘yan Najeriya kuma ana tsare da su ne saboda an kama su da laifin safarar miyagun kwayoyi da sauran munanan laifuka daban-daban.
Ya ce a zaman yanzu akwai kimanin ‘yan Najeriya 600 da ke tsare, saboda sun zarce wa’adin da aka dibar masu zu yi a cikin kasar Chana.
A karshe ya bayar da shawarar cewa duk dan Najeriya mai son zuwa kasar Chana, to ya tabbatar da cewa ya san ka’idojin zama kasar da kuma kasancewa idan ya je zai rika kiyaye tsauraran dokokin su.