TSORON DAUKAR FANSA: Kisan Bafulatani a Ekiti ya tada hankalin Gwamna Fayose

0

Gwamnan Jihar Ekiti, Ayo Fayose na can na kokarin yayyafa wa wata wutar fitina ruwa, tun bayan kashe wani Bafulatani mai suna Babuga Dengi da aka yi a kauyen Oke Ako da ke cikin karamar hukumar Ikole ta jihar Ekiti.

Rahotanni sun tabbatar da cewa a tsakar daren Talata gwamnan ya kira taron gaggawa domin kauce wa dagulewar al’amarin.

Fayose ya ce wasu kabilar Tivi ne da ke noma a yankin su ka yi kasassabar kashe makiyayin.

Gwamnan ya shaida wa shugabannin Fulani da na Tivi mazauna jihar a ranar Laraba cewa ko shakka babu sai an fito da wanda ya kashe Bafulatanin domin a hukunta shi.

“Ni ba zan yarda wani ko wata kabila ya kashe Fulani a jihar Ekiti ba.” Inji Fayose.

Share.

game da Author