Gobara ta tashi a kasuwar Yola

0

Babbar kasuwar Yola ta jihar Adamawa ta kama da wuta a jiya Laraba da dare. Amma rahotanni sun ce jami’an Hukumar Kashe gabara sun samu galabar kashe wutar.

Babban jami’in hukumar, Adamu Abdullahi, ya tabbatar cewa jami’an sa sun kashe wutar, wadda ya ce ta tashi ne daga wani injin nika ko na markade a cikin kasuwar.

Ya ce wutar ta ci wani sashe na masu sayar da kayan hatsi da kuma bangaren masu nika da markade.

Ya kara da cewa ba a samu asarar rai ko daya ba, kuma babu rahoton wani da ya ji mummunan ciwo.

Share.

game da Author