A yau ne kotu dake Karmo, Abuja ta yanke wa Moammed Salifu hukuncin bulala shida saboda damun kwabta da hayaniya da yake yi a unguwan.
Lauyan da ya shigar da kara Dalhatu Zannah ya ce a ranar 13 ga watan Janairu da misalin karfe 9 na dare ‘yan sanda a Karmo sun kama Mohammed ya na ta tangaririwa a unguwa yana ife-ife shi kadai wanda hakan na hana mutane barci.
Zunnah ya ce bayan ‘yan sandn sun kama shi ne suka gane cewa taban wiwi ne da ya sha take aiki a kwakwalwar sa.
Shi kuwa Mohammed kafin kotu ta yanke masa hukunci ya roki sassauci wanda haka ya sa alkalin kotun Abubakar Sadiq ya sa a tsula masa bulala shida.