Tsakanin Kwankwaso da Lado, Daga Ashafa Murnai

0

Yanzu dai maganganun da ’yan siyasa ke ta yadawa cewa Sanata Lado, wanda ya taba wakiltar Kano ta Tsakiya zai koma APC daga PDP, to ta tabbata, domin dai yau an yi bikin canjin shekar ta sa a Kano, shi da mutanen sa kimanin 5,000 kamar yadda aka rika yayatawa.

Abin da kuma ya rage na biyu, shi ne labarin da ke ta yawo a kasar nan, wai, wai, wai fa, Ganduje ya kulla wa Kwankwaso tsiya, za a hana shi takarar Sanata a karkashin APC, a bai wa Lado a 2019. Tunda dama shi Kwankwaso ne ya kayar da Lado a 2015.

Ganin yadda mabiya ko na ce magoya bayan APC ke ta murnar komawar Lado a cikin jam’iyyar su, a gefe daya kuma wasu da dama masu nazarin siyasar Kano da ta kasa baki daya na ganin cewa karbar Lado shi ne babban gangancin da APC ta fara yi a farkon shekarar nan. Da dama na ganin tamkar jam’iyya mai mulki ta luma wa cikin ta wuka ne a inda babu likita a kusa.

Babbar matsalar APC, ita ce, su mulkin ne kawai a gaban su, amma ba yadda za su kama zaren siyasa su ja shi da zawo ba.

Tun daga Shugaba Muhammadu Buhari da sauran jiga-jigan APC sun zuba ido ana tabka kazamin rikici a APC a jihar Kano, jihar da Buhari ya samu ruwan kuri’u milyan a biyu kadan ke babu. Amma sun syi tsaye galala da baki, su na kallo, sun kasa sasanta Gwamna Abdullahi Ganduje da Sanata Rabi’u Kwankwaso.

An yi ittifakin cewa duk da irin cika-bakin da Ganduje ke yi, to Buhari zai iya tankwara shi. A maimakon jiga-jigan APC su yi wa Ganduje taron-dangi, su dakatar da shi daga yin gaba da Kwamkwaso, sannan su nuna masa muhimmancin karfi da tasirin APC a siyasar Kano, sai su ka gwammace kwaryar jam’iyyar ta fashe gida biyu, Ganduje ya rike sakaina daya, Kwankwaso ma ya rike tasa sakainar daya.

Matsalar APC babba a nan, ita ce maida Kwankwaso saniyar-ware da ta yi, sannan kuma ta na kallon kanta a matsayin ta na mai mulki a hannu, to kamar ta zama mai-takalmin-karfe, kowa ta taka, to ya taku. Wannan kuwa kuskure ne wanda idan ba ta gaggauta yin gyara ba, to nan gaba kadan za ta ciji yatsa saboda da-na-sanin da za ta yi, watakila ma saboda zafin cizo har sai yatsan ya gutsure.

Akwai abubuwan duba da idon basira a wannan kakudubar APC a Kano. Amma abin mamaki sai idon APC ya rufe, mai yiwuwa saboda jam’iyyar ba ta jin zafin ‘Buhariyyar’ da ke jijjiga gabobi da aljifan talakawa. Dama ita jam’iyya mai mulki ai ba za ta san ana tsadar kayan masarufi ko wani abu wai shi man fetur da tashin dala ba. Ga wasu abubuwa kadan nan a kasa:

KWANKWASO DA LADO A KAN SIKELI

APC ta yi babban sakacin barin rikicin Ganduje da ubangidan sa Kwankwaso ya kai munin da har ya kai ta ga rungumar Sanata Lado. A Kano Buhari ya samu kuri’a milyan biyu ba kadan, fiye da kowace jiha a kasar nan. Don me zai bari karfin jam’iyyar ya susuce?

Bai kamata a daidai lokacin da karfin jam’iyyar APC ke ta raguwa kamar kudin guzuri a jihohin Taraba, Filato, Adamawa da Benuwai, wato jihohin Middle Belt ba, sannan kuma jam’iyyar ta zuba ido a sa zarto a gigare mata kafa daya a jihar Kano, inda ta fi karfi ba.

Gangaci muraran shi ne dan jam’iyyar APC ya raina karfin Kwankwaso da karfin mabiyan sa. Shi ne dan takarar da ya zo na biyu bayan Buhari a zaben fidda-gwanin APC a 2014. Ko an manta yawan kuri’un da ya samu bayan Buhari?

Kwankwaso ne Sanatan da ya fi kowane sanata kakaf na kasar nan samun yawan kuri’u a zaben 2015. Ashe kuwa sanatan da ya ke da kuri’a 758,383, idan ma ka raina karfin sa, to ka rudi kan ka kawai.

Sanata Lado da APC ta rungumo, kuri’a 205.809 kacal ya samu a gabzawar da suka yi da Kwankwaso a zaben 2015. Wato Kwankwaso ya yi mata ratar kuri’u 550,000 kenan.

Ta yaya za ka yi gangancin fada da mai kuri’a 758,383, sannan ka tafi ka na bugun-gaba ka kinkimo mai jama’a 205,809, kuma daga cikin su mutum 5000 kacal su ka biyo shi su ka canja sheka tare da shi?

Ko shakka babu Lado ya yi nasa tashen a Kano, musammam wajen raba wa jama’a dan hasafin da Allah ya ci-da mai rabo samu daga hannun sa. Shi ya sa ma ake masa lakabi da ‘Ladon Alheri.’ Amma ai da alherin nasa da komai ya samu kuri’a 295,809 a zaben 2015, inda Kwankwaso ya kada shi.

A wannan nazari da nayi a cikin kwanaki uku da suka gabata, sun tabbatar da cewa dubban daruruwan masoya Kwankwaso sun dinka jar hula a Kano domin tarbar Kwankwaso a Kano. Dubun dubatar masoyan sa sun dinka farin yadi ko farar shadda. Dubbai sun sayi jajayen takalma domin a yi ankon bikin tarbar Kwankwaso.

Ga mai hankalin siyasa, wannan ya nuni da cewa Kwankwaso da karfin sa gagau har yanzu, kuma irin ra’ayin akidar da ake nunawa a bin sa, ya na nuni da cewa akida ce, ba ra’ayi ba ne, kuma ba don kudi ake biye da shi ba. Mai irin wannan mabiya ko masoya kuwa, ko jam’iyyar huce-haushi ya kafa, to zai iya yin tasirin da ko bai yi nasara ba, to zai iya yin illar da shi da masu adawa da shi a su yi ragas, biyu babu kenan!

Binciken da nayi a Abuja daga ranar Litinin zuwa yau Lahadi, ya nuna cewa kafin ka ga fastar hoton Buhari a Keke NAPEP daya, ka ga fastar hoton Kwankwaso a guda uku. Sannan kuma babu unguwannin cikin birnin Abuja da za ka shiga ba ka ga matasa ‘yan ci-rani da mazauna birnin, musammam Kanawa sanye da jajayen hulunan Kwankwaso ba.

Sauran garuruwa ma irin su Suleja, Deidei, Zuba, Kubwa, Dutsen Alhaji, Bwari, Lugbe, Gwrimpa duk za ka rika ganin masu baburan acaba sanye da hular Kwankwaso, ko kuma direbobin KEKE NAPEP sanye da jajayen huluna.

Kun san kuwa irin wadannan matasan, da an ce maka zabe ya karato, za ka rika ganin zugar su a kan babura ko kan talbodin tireloli da motocin katako su na tafiya kauyukan su domin su dankwala kuri’a.

Share.

game da Author