Majalisar Tarayya ta bayyana cewa duk wata kisisina da kulle-kullen cire Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki, ba za ta yi nasara ba, saboda mambobin majalisar dattawan ba za su taba tsige shi ba.
Kakakin yada labaran majalisar ne, Sanata Sabi Abdullahi ya bayyana haka a lokacin da ya ke magana da manema labarai a karshen makon nan.
Abdullahi ya yi nuni da cewa Saraki ya kawo zaman lafiya a majalisa, kuma majalisar a zamanin sa ta zauna daram, ta na gudanar da ayyukan ta ba tare da wata tangardar cikin gida ba.
Kakakin ya ce idan aka duba yadda Sanata Saraki ke shugabancin Majalisa, za a fahinci irin yadda zamantakewar zaman lafiya ya samu a cikin kasar nan, ba ma a cikin majalisa kadai ba.
“Babu mai iya tsige Saraki. Mu ne mu ka zabe shi, kuma ba mu da wata niyya ko dalilin tsige shi. Tun daga farko ba son Saraki makiyan sa su ke yi ba. Abin da na ke fadi shi ne, mu ‘yan majalisar dattawa ne ke da hakkin zabar shugaban mu, kuma mun rigaya mun zabi Saraki.”