Darekta a hukumar Fansho ya sheka lahira bayan an mika masa takardar sallama

0

Gwamnatin jihar Kogi ta bayyana cewa ta kori tsohon shugaban hukumar fansho na jihar Alphonsus Ameh a dalilin kama shi da laifi wawushe kudaden hukumar sama da naira miliyan 225.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta rawaito cewa Ameh ya rasu ne a babbar asibiti a Lokoja kwanaki kadan bayan an mika masa takardar sallamar sa.

Mai taimaka wa gwamnan jihar kan yada labarai, Petra Onyegbule, ta fadi cewa kwamitin da gwamnati ta kafa don yin da bincike kan badakalar hukumar fansho na jihar ne ta tona masa asiri sannan ta bada shawarar a sallame sa daga aikin sa.

A zaman da kwamitin tayi shi marigayi Ameh ya tabbatar wa kwamitin cewa ya karbi wadannan kudade ne a matsayin na goro don bikin kirismeti. Bayan haka ya bukaci ayi masa sassauci don ya fara biya ganin kuma cewa shi tsohon ma’aikacin hukumar ne.

Ya ce miliyan biyu kacal ya karba a rabon kudin.

Petra ta ce furicin da Ameh ne ya yi ne ya tabbatar wa kwamitin cewa lalle ya aikata hakan sannan ta bada shawarar a sallame shi daga aiki tare da wasu ma’aikata 4 da aka kama da laifin aikata wannan laifi tare da Ameh.

Share.

game da Author