Ba mu sa a kamo shugaban kamfanin BUA ba – Rundunar ‘yan sandar

0

Kakakin Rundunar ‘yan sanda na kasa Moshood Jimoh ya bayyana cewa, sam sam ba shi da masaniya kan cewa da akayi wai rundunar ‘yan sandan ta ce a kamo mata shugaban kamfanin BUA, Yusuf Binji.

Da ya ke fadin haka ta wayar tafi da gidan ka, Moshood ya ce ba su da masaniya kan haka sannan basu san cewa wai an kai wa gwamnan jihar Edo hari ba da yaje filin aiki na BUA.

Ya kara da cewa idan har ma an kai wa gwamnan Edo hari, rundunar ‘yan sanda za su gudanar da bincike akai.

Idan ba a manta ba ana ta kai ruwa rana tsakanin kamfanin Dangote, da Bua kan wane ne mai asalin mallakin filin hako sinadarin hada siminti dake jihar.

Gwamnatin Edo sun ce Yusuf Binji ne ya shirya wasu matasa su kai wa gwamnan hari da ya kai ziyara filin hako duwatsun.

Share.

game da Author