El-Rufai ya yi wa kwamishinonin sa garambawul, ya sallami daya, ya Karo biyu

0

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya canza wa wasu kwamishinonin sa ma’aikatu sannna ya sallami daya, ya kuma Karo sabbi biyu.

Kwamishinan albarkatun ruwa na jihar, Injiniya Suleiman Aliyu ne bai sha ba a garambawul din. Gwamna El-Rufai ya yi masa addu’ar fatan Alkhairi.

Sabbi da aka nada sun hada da Ruth Alkali, ma’aikatan cinikayya, da yawon shakatawa.

Ibrahim Hamza kuma an nada shi sabon kwamishinan albarkatun ruwa.

Farfesa Kabiru Mato kuma ya koma ma’aikatan kananan hukumomi daga ma’aikatan ayyukan gona.

Ja’afaru Sani na ma’aikatan kananan hukumomi ya koma ma’aikatan ilimi na jihar.

Balabara Aliyu-Inuwa daga ma’aikatan bunkasa karkara zuwa ma’aikatan Ayyuka.

Hassan Mahmud daga ma’aikatan Ayyuka zuwa ma’aikatan bunkasa karkara.

Sauran kwamishinonin na nan a ma’aikatan su.

Share.

game da Author