TABARMAR KUNYA: Gwamnati ta ce Dala Biliyan 1 din nan ba ta yaki da Boko Haram kadai ba ce

0

Gwamnatin Tarayya ta yi saurin yin kwana cikin gaggawa ba shiri, inda ta bayyana cewa tsabar kudin nan dala biliyan daya da gwamnoni su ka amince a kashe, to ba a kan Boko Haram za a kashe kudin gaba daya ba.

Gwamnatin Buhari dai ta shiga tsomomuwa a daidai lokacin da aka kai karshen wannan shekara, tun bayan sanarwar da aka yi cewa gwamnonin kasar nan sun amince tarayya ta cire dalar amurka daga asusun rarar man fetur har kwatankwacin naira biliyan 360 domin a yi yaki da Boko Haram da kudin.

Gwamnan jihar Zamfara ne, Abdul’aziz Yari ya bayyana haka, a matsayin sa na Shugaban Kungiyar Gwamnonin Kasar nan a makon da gabata, jim kadan bayan fitowar su daga taron majalisar gudanarwa a fadar Aso Rock.

Tun daga ranar da aka yi wannan jawabi ne ake ta caccakar gwamnatin Muhammadu Buhari, wadda a baya ta ce ta kakkabe Boko Haram a kasar nan.

Idan ba a manta ba, a farkon shekarar nan, har wani littafin Hadisai aka kai wa Buhari har fadar sa, tare da tuta, aka ce masa ai Shekau ne ya ari takalmin kare, ya arce ya bar hadisi da tutar.

Amma kuma sai ga shi a makon da ya gabata ana shirin cire naira biliyan 360 domin a sayo makamai a yi yaki da Boko Haram.

Nan da nan gwamnan Ekiti, Ayo Fayose ya ce kudin za a dai cire su ne kawai domin yakin neman zaben 2019. Yayin da wasu da dama kuma su ka tafi a kan ra’ayin cewa ita ma gwamnatin Buhari ta kamfato tata harkallar ta ‘Malam ya ci kudin makamai.’

Akwai ma wadanda ke cewa ai dama ana yawan maganar su ’yan siyasa ba su son rikicin Boko Haram ta kare, domin ita ce babban bututun da ake zurara makudan kudade, idan sun zurare, sai su tare su kwashe.

Haka nan kuma, PDP ta yi amfani da wannan dama ta rika caccakar gwamnatin APC, ta na mai cewa ita ma APC ta kusa kirkiro na ta “Dasukin Buhari” kenan.

To amma kuma a yau Talata, Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, ya fito ya yi ‘waske-malam’, inda ya ce wadannan kudi ba kan Boko Haram ne kadai za a kashe su ba, har da sauran matakai da fannoni na tsaro.

Ya na mai cewa duk wata harkar da ta shafi tsaro ne za a yi amfani da kudin, ba kan Boko Haram kadai ba, har da tsaron da ya shafi, cikin al’umma, unguwanni, karkara, kauyuka, birni da kowane bangare na matsalar tsaron kasar nan.

Osinbajo ya yi wannan bayani ne a wurin taron sanin makamar aiki da ake yi wa sakatarorin gwamnatin jihohi da na tarayya, yau Talata, a Abuja.

Share.

game da Author