2017: An kama miyagun kwayoyi da ya kai naira biliyan 4 a Kano

0

Gwamnatin jihar Kano ta ce ta kona miyagun kwayoyi da ta kama a wannan shekara da suka kai na naira biliyan 4.1.

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ne ya sanar da haka a zaman da kwamitin majalisar dattijai take yi don binciken yadda amfani da irin wadannan kwayoyi ya zama ruwan dare a musamman jihohin arewacin kasar nan.

Ganduje wanda mataimakin sa Hafiz Abubakar ya wakilta ya ce sun kwato wadannan miyagun kwayoyin ne daga sassa dabam dabam na jihar.

Daga karshe ya mika godiyar sa ga majalisar dattijai bisa wannan kokari da ta keyi domin ganin an kawo karshen wannan mummunar dabi’a da yara musammam suka fada ciki.

Share.

game da Author