RASHIN ALBASHIN WATA BIYU: ‘Yan sanda sun yi zanga-zanga

0

Wasu jami’an ‘yan sanda da ba su ga albashin su na wata biyu a asusun ajiyar su na Bankin Micro Finance a Yola ba, sun gudanar da zanga-zanga.

‘Yan sandan dai sun ce ba su ga albashin su na Oktoba da Nuwamba ba, ga shi kuma Disamba ta kusa karewa.

Wasu jami’an da suka yi magana amma su ka nemi a boye sunayen su, sun bayyana cewa ya kamata a gaggauta daukar matakin da ya dace a dauka, don a biya su hakkunan su, domin su na cikin rayuwar kunci sosai.

“Sauran abokan aikin mu da ke karbar albashi a wasu bankuna duk sun karbi na su babu wani bata lokaci, kuma a kan kari. Amma mu an bar mu sai je-ka-dawo ake ta yi mana.

Yayin da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa, Othman Abubakar ya ce ba shi da hurumin cewa komai a kan wannan magana.

Amma Manajan Bankin Yusuf Haruna, ya ce har yau ba a bai wa bankin kudaden da su ka kamata su biya ‘yan sandan albashin su ba.

‘Yan sandan sun je kofar bankin amma ba sanye da kaki ba, sun isar da kukan su, daga can kuma su ka nufi hedikwatar ‘yan sanda a Yola, inda bayan sun isa aka ba su umarnin to su tafi haka nan tunda an saurari kukan su.

Share.

game da Author