Kofur na ’yan sanda ya bindige direban bas a inda su ke tare hanya

0

Rundunar ’yan sandan jihar Ekiti, ta cafke wani kofur na ‘yan sanda a dalilin bindige wani direban bas har lahira a ranar Talata da yayi a wajen da suke tare hanya.

Jami’in Hulda da Jama’a na jami’an tsaron, Alberto Adeyemi ne ya shaida wa ‘yan jarida haka a ranar Laraba,inda ya kara da cewa abin ya faru ne a garin Oye Ekiti, cikin karamar hukumar Oye.

Ya ci gaba da cewa a daidai inda jami’an tsaro suka yi shinge ne a hanya abin ya afku.

“A zaman yanzu dai ya na fuskantar shari’a ta mu ta nan cikin gida, kuma da an kammala, za a kore shi kawai daga nan kuma a maka shi kotu.”

Wani wanda aka bindige direban bas din a idon sa, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai, NAN cewa direban ya dauko fasinjoji ne daga garin Ikara da ke cikin jihar Ondo.

“Motar ta kwace wa direban a lokacin da aka dirka masa bindiga, ta yi cikin daji, ta fadi. Fasinjojin da ke ciki kuma su ma sun samu raunuka da dama.

Share.

game da Author