Manajan Daraktan Kamfanin Kula da Albakatun Mai, NPMC, Umar Ajiya, ya bayyana cewa za a fara kwace dukkan wani man fetur da ka kama an boye a gidajen main a fadin kasar nan.
Ajiya ya kara da cewa, duk wanda aka kama, to nan take za a rika rabas da shi kyauta ga motocin ko direbobi.
Ya kara da cewa bayan sun kewaya gidajen mai shida a Abuja tare da jami’an NNPC, ya na mai cewa janyewar dogayen layin mai a Abuja, shi ne irin kokari da jajircewar da dukkan hukumomin da ke da ruwa da tsaki su ka nuna wajen ganin man ya wadata kan lokaci.
Ya ce sun rika yin aiki ba dare, ba rana awa 24 a dukkan gidajen mai na su.
Ajiya ya bayyana cewa tun asalin wannan matsalar mai ta kwanan nan, shi ne wani rudu da aka fara watsawa cewa za a kara kudin mai, wanda tun a ranar hukumar su ta karyata wannan jita-jita.
“Wannan ne ya sa mutane suka rika tururuwa su na sayen mai, ko don su yi tanadi ko kuma su tara su yi cuwa-cuwa.