Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kebbi Ibrahim Kabiru yace tsakanin watannin Janairu zuwa Disambar 2017, rundunar su ta kama ‘yan fashi da makamai 41 sannan ta kwato makamai 12 daga hannun su.
Ya ce a yanzu haka ‘yan fashin na tsare a kurkuku sannan za su ci gaba zama a kurkukun har sai bayan an gama sauraron kara da aka shigar akan su a kotu.
Kabiru ya kuma kara da cewa a cikin tsawon wadannan watannin rundunar ta kama barayin motoci da babura 7 sannan suma sun shigar da kara a kotu.
Ya ce sauran kayan da suka kwato daga hannun barayin sun hada da motoci 6 da babura 16.
” Mun kuma mayar da garken shanu 131 wa ainihin masu su.”
Kabiru ya yi kira ga mutanen jihar da su ci gaba da ba jami’an tsaro hadin kai domin kawar da masu aikata irin wannan miyaguna aiyukka a jihar.
Discussion about this post