KIWON LAFIYA: Mata masu ciki 100 ne suka rasa rayukan su a jihar Zamfara

0

Ma’aikacin babban asibitin gwamnati dake Gusau jihar Zamfara, Abubakar Danladi ya ce a shekaran 2016 jihar ta rasa mata masu ciki 100 sanadiyyar matsaloli dabam dabam.

Danladi ya bayyana haka ne a taron da kungiya mai zaman kanta ‘Advocacy Nigeria Network’ ta shirya kan gudunmawar da kungiyoyin kare hakkin jama’a CSO da gidajen jaridu za su iya bada wa game da shawo kan wannan matsalar.

Danladi ya ce Najeriya na daya daga cikin kasashe a duniya da suka fi fama da mutuwan mata masu ciki musamman a arewacin kasar nan.

Ya ce a Najeriya matsalolin da ke yawan kawo ajalin mata masu ciki sun hada da hawan jini da yawan sinadarin ‘Protein’ da akan samu a fitsarin mace mai ciki wato ‘Eclampsia’ da turanci da zuban jini.

Ya ce a zahiri bai kamata irin wadannan matsalolin su dunga fin karfin likitoci ba da ma’aikatan jinya a asibitocin kasar nan ba amma saboda rashin ma’aikata, rashin magunguna da rashin kayan aikin ne ke kawo hakan.

Daga karshe Danladi ya yi kira ga kungiyoyin CSO da gidajen jaridu na Najeriya da su yawai ta tunatar da gwamnati kan muhimman cin kula da mutanen kasar nan.

Share.

game da Author