Na yi da-na-sanin rashin maida Jos babban birnin Najeriya – Yakubu Gowon

0

Tsohon Shugaban Najeriya na mulkin soja, Yakubu Gowon, ya na yin da-na-sanin rashin maida Jos matsayin babban birnin Najeriya.

Gowon ya ce ya ki aiwatar da haka ne don kada a ce ya cika tsananin nuna son yankin sa ko kuma yi wa sauran yankin kasar nan mugunta.

Gowon ya yi mulki har tsawon shekaru tara, daga 1966 zuwa 1975, amma ya ce ya na da-na-sani da bai maida Jos ta zama babbar birnin Najeriya ba.

Gowon ya yi wannan bayani ne a wurin bikin cika shekara 26 da maida babban birnin tarayya daga Lagos zuwa Abuja.
Taken bikin nuna kayan shi ne ‘Shi ne daga Barikin Dodan zuwa Fadar Aso ROCK.’

Ya ce saboda ya na kallon garin Jos ya yi kusa da mahaifar sa, shi ya sa bai maida shi ya zama cibiyar Nijeriya ba.

Gowon ya kara da cewa har ya sauka bai yi amfani da karfin mulki ya tara dukiya ba.

Ya ce a zamanin mulkin sa aka fara bijiro da batun sauya babban birnin Najeriya daga Lagos, cikin 1974.

“Amma sai wadanda ke da shauki da kishin sauya babban birnin, kamar irin su Marigayi Murtala, su ka ci gaba da shirin bayan ba na mulki.”

“ Daga cikin dalilan da su ka sa na so a maida babban birnin a can, shi ne yadda Jos ke da kyau. Kowa na san zai yadda cewa Jos da kewayen ta wuri ne mai kyau sosai. Amma ganin ya yi kusa da mahaifa ta, sai na yi gudun kada a ce na nuna son kai, ko na fifita wani yanki.”

“Neman wani wurin da ya ne har ya kai ni inda Abuja ta ke yanzu, kuma na ga Abuja ta yi sosai.”

Gowon ya nuna takaicin sa cewa duk da shi ne wanda ya fara nuna Abuja ce ta fi dacewa ta zama sabon babban birnin kasar nan, an yi ta gine-gine, har gwamnati ta kafu a Abuja, amma ba a sa wa wani titi ko gini sunan sa ba, har sai da ya yi wa tsohon shugaban kasa, Babangida korafi tukunna.

Ya ce an yi masa haka ne, domin akwai wasu jami’an gwamnti da ke kusanci da gwamnati, masu yi masa sharrin cewa akwai hannun sa a mutuwar Murtala.

Share.

game da Author