An sake kai wa Magu hari har gida

0

A karo na uku, wasu maharan da ba san ko daga ina su ke ba, sun yi wa gidan Shugaban Hukumar EFCC dirar-mikiya, har suka kashe dan sanda daya.

Jiya Talata ne cikin dare da misalin 10 na dare, aka kai masa harin har gida, a Karshi, wani wani gari da ke wajen Abuja.

Wadanda su ka kai harin, sun samu nasarar kama dan sanda daya da kuma wani mai aikin gidan, suka daure su tamau da igiya.

An yi musu dukan tsiya, har sai da dan sandan ya kai ga mutuwa.

Dama a baya an taba kai hari gidan aka yi masa cakarkaca, a lokacin da ake aikin gidan, kafin a kammala shi.

Cikin Agusta kuma an je an bude wuta a ofishin Magu, inda maharan su ka yi bata-kashi da masu tsaron kofar shiga ofishin.

Wancan hari da aka kai masa ne ya sa aka kara masa yawan masu gadin sa, kamar yadda wata najiya ta bayyana wa PREMIUM TIMES.

Ba a san dalilin kai wannan hari ban a jiya Talata ba, amma dai an yi awon-gaba da shanu biyar da tumakan da ba san yawan su ba, da yake ana kiwon dabbobi a gidan.

PREMIUM TIMES ta samu labarin ana can ana bincike, sai dai kuma an yi kokarin jin ta bakin Magu ko kakakin yada labaran sa, amma abin bai yiwu ba.

Ba Magu ne aka fara yi wa irin wannan ba, a wata hira da marubucin wannan labara ya taba yi da tsohuwar Shugabar Hukumar EFCC, Farida Waziri, ta shaida masa irin yadda aka yi ta kokarin neman halaka ta, ta hanyar tsibbace-tsibbace, asirai ko makaru.

“Akwai ranar da na dawo daga aiki na samu an jefo wasu tulin layu da guraye a cikin gida na. Kuma ta bayan gida aka jefo su.

“Sannan akwai kuma ranar da zan tafi aiki da safe, ni dai na san ni da kaina na rufe kofar falo na, na sa makulli a jaka na fita. Da na dawo kuma, ni da kaina na sa makulli, na bude, na shiga na kulle. Na ajiye jaka, na wuce na je na yi alwala. Ina zuwa daidai inda na ke yin sallah, sai kawai na ga tulin layu, guraye da wasu rakwancamai na karhunan asiri an tule su a gaban dardumar da na ke sallah.”

Ta ce har a lakacin da ake hirar da ita ba ta san ta yadda aka yi aka shiga har aka jibge mata layun a cikin falo, inda ta ke sallah ba.

Share.

game da Author