Ministan Harkokin Sufuri, ya shawarci takwarorin sa ministoci da ke cikin gwamnatin Muhanmmadu Buhari, da su daina dora laifuka a kan gwamnatin Jonathan haka nan.
Amaechi ya ce lokaci ya yi da wannan gwamnatin da jami’an ta su maida hanhali a kan cika alkawurran ababen more rayuwa da ayyukan ci gaban kasar da suka yi wa jama’a alkawarin za su gudanar musu.
Ya ci gaba da cewa idan ana gudu ana waiwaye, to fa babu inda za a kai a cikin hanzarin da ake so a cimma.
“Ni fa na yarda da masu cewa mu daina sukar gwamnatin da ta gabata haka nan, mu maida hankali ga abin da ke gaban mu. Haka jaridar The Nation ta ruwaito Amaechi na bayani a wata ganawar da ya yi ranar Talata a ofishin ta.
Daga nan sai ya nuna takaicin rashin ababen more rayuwa ko ci gaban kasa a Najeriya, inda har ya fifita karamar kasa kamar Singapore a kan Najeriya.
“Yanzu fa ko motsi wadanda suka ci gaba suka yi, to fasaha ce ke motsa su. Na gaba sun ci gaba, sun yi wa na baya fintinkau. Don haka tilas mu hanzarta tashi tsaye domin mu kamo wadanda suka yi mana tazara.” Inji Amaechi.
“Har cewa fa suka yi nan da ‘yan shekaru masu zuwa za su kirkiro mota wadda ba ta da direba. To mu ma mu kokarta mu kai duk inda ya kamata a ce mun kai.
“ Amma hakan ba zai yiwu ba sai mun kara kaimin bayar da muhimmanci ga fasaha ta kirkire-kirkiren zamani, wato ICT.” A ta bakin Amaechi.