Babban dan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Yusuf Buhari, ya karya kafadar sa a wani hadarin babur da yayi a unguwan gwarimpa dake Abuja, daren jiya.
Kamar yadda fadar shugaban kasa ta sanar bayan kafadar da ya gurde, ya samu rauni a kan sa.
Wannan hadari dai ya auku a unguwar Gwarimpa da ke Abuja.
Yanzu dai yana kwance a wani asibiti dake Abuja ana duba shi.