1 – ADAM ZANGO
Adam Zango na daya daga cikin ‘yan fina-finan Hausa da suka yi fama da wasu kalubalai.
Idan ba a manta ba a watan Nuwambar 2017 Adam Zango ya fito a fusace inda ya ke kalubalantar duk wanda yake cewa wai yana yin tsafi da kuma harkar bin maza.
Adam a shafin sa na ‘Instagram’ ya nuna fushin sa matuka game da hakan sannan ya ja kunen mutane da su daina haka ko kuma su sa kafar wando daya da shi.
Bayan haka kuma Adamu ya gargadi masu gyra masa rubutun sa na turanci da su dai na haka. Ya ce baya nayi bane don ya burge sai don ya isar da sako ga masoyan sa da basu jin turanci.
2 – UMMAH SHEHU
Ita kuma Umma Shehu ta yi fama ne da zargin rashin samun kyakkawar ilimin adinin ta na musulunci.
Anyi ta yin cecekuce tun bayan tabargazar da ta yi a wata hiran da Momoh na gidan Talabijin din Arewa 24.
Momoh ya yi mata wasu ‘yan tambayoyi ne game da adinin musulunci wanda mutane basu gamsu da shi ba.
Sakamakon hakan ya sa dole Umma Shehu ta fara gudun mutane.
Amma daga baya Ummah ta ce ‘koda haka ya faru hakan bai hana ta zama musulma ba musamman yadda hira ce kawai suka yi amma ba hiran tambayoyin adinin musulunci ba’’.
3 – RAHAMA SADAU
Fitowar Rahama Sadau a wani bidiyon wakar wani mawaki mai suna ‘Classiq’ a 2016 ne farkon sanadiyyar matsalolin da Rahama Sadau ta yi fama da su a farfajiyyar fina-finan Hausa har a 2017.
Sakamakon haka ya sa Rahama ta rubuta wa MOPPAN wasikar neman afuwa game da dakatar da ita da MOPPAN tayi.
An yi ta kai ruwa rana tsakanin Rahama Sadau da kungiyar MOPPAN inda har yanzu bata sanar ko ta yafe mata ba ko bata yafe mata ba.
A yanzu haka Rahama tana ci gaba da shirya fina-finan Hausa da wadansu harkokin ta a farfajiyar.
Discussion about this post