Ma’aikatan gwamnati basu dawo aiki ba duk da kammala hutun kirismeti da gwamnati ta bada na ranakun litinin da talata a babban birnin tarayya, Abuja.
Kamfanin dillancin labarai ya bayyana cewa a zagaye da yayi na ofisoshin gwamnati yau Laraba, sama da kashi 80 bisa 100 na ofisoshin ma’aikata a kulle suke.
Wani da ya zanta da NAN, ya ce hakan na da nasaba da tafiye tafiye da ma’aikata suka yi zuwa kauyukan sa domin shagulgulan bikin kirismeti.
“Ko da yake bakin wahalar mai da ake fama dashi bai kau ba duk da haka mutane sun ganganda sun tafi ganin iyaye da kakanni a Kauye. Kafin ka ga wani abu ya kankama sai watan janairu tu kuna.”
Da aka zaiyarci asibitoci kuwa, abin ba haka bane domin ma’aikatan kiwon lafiya aiki bayan hutun kirismeti.
Discussion about this post