An yi kuskure a sunayen da fadar shugaban kasa ta fitar, amma za a gyara – Garba Shehu

0

Fadar shugaban kasa ta warware cecekucen da ake ta yi tun bayan fitar da sunayen sabbin nadin da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi na ma’aikatun gwamnatin tarayya.

A wannan sunaye da aka fitar ranar Juma’a an sami sunayen wasu da suka dade da rasuwa, wasu kuma duk ‘ya’yan jam’iyyar PDP ne sannan kuma wasu an maimaita sunayen su a wasu ma’aikatun.

Garba Shehu da ya sa hannu a takardar ya ce babu wanda ya fi karfin yin kuskure a aikin sa. Ya ce kuskure ne aka samu wajen hada sunayen.

” Abin da na ke so ku gane shine, an dade da fara hada wadannan sunaye. An fara ne tun lokacin Babachir Lawal na sakataren gwamnatin tarayya.

” Da aka ci zabe a 2015, shugaba Buhari ya umurci jam’iyyu a jihohi su kawo sunayen mutane 50 domin nada su a mukaman gwamnati. Daga baya gwamnoni suka harzuka suka ce ana yin abin ba da su ba, daga nan sai aka sake yi wa abin garambawul. Bayan Babachir ya tafi sabon sakataren gwamnati Boss Mustapha kuma bai taba komai ba akan abinda ya iske. Da aka bukaci a aiko da sunayen domin Buhari ya amince da su ya miko su haka.”

Garba ya ce babu wani abin damuwa a ciki domin kuskure ne kuma babu wanda ya fi karfin yin sa.

Ya kara da cewa nan ba da dadewa ba za gyara kuskuren da aka yi.

Share.

game da Author