Tsohon gwamnan jihar Kebbi, Saidu Dakingari ya canza sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.
Tare da tsohon gwamnan a wannan canji, mataimakin sa Ibrahim Aliyu da tsohon sakataren gwamnatin jihar Rabiu Kamba.
Bayan su akwai ‘yan majalisar wakilai da suka bi sahun tsohon gwamnan da makarraban sa da suka hada da Sani Kalgo, Abdullahi Dan-Alkali, Alhaji Haruna Hassan da Halima Tukur.
Gwamnan jihar Abubakar Bagudu, da ministan Shari’a Abubakar Malami, sun yabi wannan kokari na tsohon gwamnan da makarraban sa inda suka ce hakan yayi daidai sannan yazo akan lokaci.