BANKWANA: Abubuwa 50 da suka faru a 2017

0

1. Shekarar jinyar Shugaba Muhammadu Buhari.

2. Shekarar yawaitar garkuwa da mutane.

3. Shekarar yawan harbe ‘yan fasa-kwauri da jami’an kwastan su ka rika yi.

4. Shekarar rikicin Fulani da manoma.

5. Shekarar yawaitar hadurran motoci.

6. Shekarar tsadar kayan masarufi.

7. Shekarar tsadar hasken lantarki.

8. Shekarar tsadar Dala da Euro.

9. Shekarar faduwar darajar naira.

10. Shekarar masu hura usur.

11. Shekarar jibga wa gwamnoni kudin Paris Club.

12. Shekarar ciwo bashi kasashen waje.

13. Shekarar ambaliya a wasu jihohi.

14. Shekarar da aka ce an kakkabe Boko Haram.

15. Shekarar kafa Kwamitocin Bincike.

16. Shekarar da beraye su ka mamaye Fadar Shugaban Kasa.

17. Shekarar da aka karya lagon Nnamdi Kanu da IPOB.

18. Shekarar cututtuka.

19. Shekarar da Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da matar sa su ka cika shekara biyu a tsare.

20. Shekarar da aka rufe filin jirgin sama na Abuja.

21. Shekarar korar malaman firamare a jihar Kaduna.

22. Shekarar fallasa bahallatsar Sanata Bukar Abba Ibrahim.

23. Shekarar yawaitawa da tsawwala wa ‘yan Najeriya haraji.

24. Shekarar yawaitar barayin shanu.

25. Shekarar harkallar kayan agajin Sansanonin ‘Yan Gudun hijira.

26. Shekarar da aka fi biyan tafiya aikin Hajji da tsada.

27. Shekarar auren Zahra, ‘yar Shugaba Muhammadu Buhari.

28. Shekarar yawaitar fyaden kananan yara.

29. Da aka karbo wasu gungun daliban makarantar Chibok.

30. Shekarar da aka ritsa Charley Boy a Kasuwar Wuse, Abuja.

31. Shekarar kashe-kashen kabilanci a Taraba da Adamawa.

32. Shekarar da kwangilar datse ciyawa ta ci rawanin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal.

33. Shekarar bankwana da wasu manya, irin su Alex Ekweme, Danmasanin Kano, Sarkin Katagum, Danfulani Suntai da sauran su.

34. Shekarar da aka yi rokon ruwa a cikin watan Ogas a Katsina.

35. Shekarar da aka sheka ruwa a cikin watan Disamba a Abuja.

36. Shekarar da jami’an ‘yan sanda su ka sace kayan gidan Tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan karkaf.

37. Shekarar da aka fi caccakar gwamnatin Buhari, ana nuna gazawa da lusarancin sa.

38. Shekarar da jam’iyyar PDP ta yi taron Gangamin Zaben Shugabannin ta.

39. Shekarar da Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya fice daga APC, ya koma PDP.

40.Shekarar da aka fi yi wa jam’iyyun siyasa da yawa rajista.

41. Shekarar da daliban da su ka kammala sakandare su ka fi rashin samun damar shiga jami’a.

41. Shekarar samar da aikin yi a tsarin N-POWER.

42. Shekarar da harkallar Abdulrashid Maina ta zubar da kimar gwamnatin Buhari.

43. Shekarar da EFCC ta fi bankadowa da kwato makudan kudade da kantama-kantaman gudajen manyan barayin gwamnati.

44. Shekarar da kotunan kasar nan ba su daure manyan barayin gwamnati ko guda daya ba.

44.Shekarar da fadar gaskiya ya nemi raba Sarkin Kano da rawanin sa.

45. Shekarar da gabar Kwankwasiyya da Gandujiyya ta dakushe kaifin APC a Kano.

46. Sufeton ‘Yan Sanda, Ibrahim Idris da Sanata Hamma Misau su ka rika kwance wa juna zani a kasuwa.

47. Shekarar da Majalisar Dattawa da Fadar Shugaban Kasa su ka casu a kan amincewa da kin amincewa da Shugaban EFCC, Magu.

48. Shekarar da kungiyar Kwallon Kafa ta Super Eagles ta yi nasarar zuwa gasar cin Kofin Duniya da za a gudanar a Rasha, 2018.

49. Shekarar da Yusuf, dan Shugaba Muhammadu Buhari ya yi hadari da babur din tsere, ya ji mummummnan rauni a Gwarimpa, Abuja.

50. Shekarar da ta zo karshe a cikin masifar tsada da kuma karancin man fetur.

Share.

game da Author