Sanadiyyar rauni daya samu a kansa da karya kafadarsa da yayi, babban dan shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Yusuf Buhari ya bar kasar nan zuwa kasar Jamus domin ganin likitoci.
Yusuf ya yayi wani mummunar hadarin babur daren Talata a unguwar Gwarimpa, Abuja, inda ya karya kafadar sa sannan ya sami rauni a kansa.
An fice da Yusuf zuwa kasar Jamus ne a safiyar Alhamis rangaranga.
Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya aika da sakon Allah kyauta ga shugaba Buhari sannan yayi kira da a taya iyalan shugaban kasan da addu’a Allah yaba Yusuf lafiya.
Allah ya bashi Lafiya.
Discussion about this post