Wani abin Al’ajabi da ya auku a unguwar Katsina Tike, dake karamar Hukumar Jada jihar Adamawa shine ganin yadda aka yanka wata kaza, sannan ta tashi abin ta ta ci gaba da tafiyar ta.
Abin dai kamar almara, yanzu kwananta biyu Kenan a tsaye bata mutu ba.
Kabiru Tukur Jada, da ya sanar wa PREMIUM TIMES HAUSA ya ce hakan ya dimauta mutanen Anguwar sannan har yanzu an zuba wa ikon Allah Ido.
Mutane dai sai tururuwa suke yi zuwa gidan da abin ya faru domin ganin ko yaya.
Sai dai wasu sun ce da an guntule kan ne a gani ko ba zai mutu. Amma duk da haka abin da ban mamaki.