Kwanaki 4 da shiga sabuwar shekara, majalisar Kaduna ta amince da kasafin kudi na naira biliyan 19 kari a kasafin 2017

0

A wata zama ta musamman da majalisar Kaduna tayi yau, ta amince da karin kasafin naira biliyan 19.2 domin kammala wasu ayyuka dake kasafin 2017 da ya hada da ayyukan noma da raya karkara da ba a samu an kammala su ba saboda rashin kudi.

Majalisar tace tayi haka ne domin a samu a kammala ayyukan da aka fara ba a kammala su ba da zaran an shiga sabuwar shekara.

Shugaban kwamitin yada labarai na majalisar Nuhu Shadalafiyaya bayyana cewa majalisar tayi haka ne domin ta samar wa mutane kudaden da suka nema na bashi domin ayyukan noma.

Ya gargade su da su yi amfani da wadannan kudade yadda ya kamata sannan sauran ayyukan da za a kammala za su amfanar da mutane musamman ‘yan kwangila da suka bar wuraren ayyukansu za su koma domin ci gaba da ayyuka.

Share.

game da Author