Adam Zango ya karrama masoyan sa a Kano

0

ZAN 2

Jarumi Adam Zango, ya karrama wasu daga cikin masoyan sa dake garin kano a wani kasaitaccen buki da yayi a Shagalinku dake Kano.

Bayan haka ya kaddamar da shirin sakin sabuwar fim din sa mai suna gwaska da zai fito ranar 1 ga watan Janairun 2018.

A bukin wasu daga cikin wadan da suka halarci taron sun sami kyautuka da ya hada da riguna, huluna da sauran su.

Jarumai kamar su Ali Nuhu, Nafisa Abdullahi, duk sun halarci bukin.

Daya daga cikin na kusa da Adam Zango, Mansur Make-up, ya bayyana wa Premium Times cewa Adam Zango ya shir wannan buki ne don nuna wa masoyan sa irin kaunar da yake musu da kuma gode musu kan kaunar da suke nuna masa.

Itama jaruma Fati SU da take tofa albarkacin bakin ta game da bukin ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa ” Adam Zango mutum ne mai kowa nasa. Abin da yayi wa masoyan sa abu ne da ya cancanci yabo. Yana da matukar kyauta da taimako. Mu kan mu Jarumai bai bar mu ba wajen ganin ka sami daukaka duk ta yadda zai taimaka.” Fati tace.

Adam ya gode wa masoyan sa da sauran abokanan aikin sa da suka halarci bukin a wata bidiyo da ya saka a shafin sa na Instagram.

ZAN 1

ZAN 4

Share.

game da Author