An kori ’yan sandan da aka kama da buhunan tabar wiwi 30

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Kogi ta kori wasu jami’an ta uku saboda an same su da laifin fataucin tabar wiwi.

Kakakin yada labaran rundunar, ‘yan sandan, William Aya ya tabbatar da wannan labari a yau Laraba a Lokoja, inda ya kara da cewa an kuma damka su ga hannun Hukumar Hana Sha da Fataucin Muggan Kwayoyi, NDLEA, kasancewa an same su da buhun wiwi har 30.

Ya kara da cewa hukumar za ta gurfanar da su a gaban kotu, tunda an rigaya an gama bincike.

Idan za a iya tunawa, ranar 7 Ga Nuwamba ne aka kama ‘yan sanda uku bisa laifin yin rakiyar motar da ta yi lodin tabar wiwi har buhu 30 a wajen garin Lokoja.

An dauki tabar ce a cikin wata mota mai lamba KN 185 LG, wadda jami’an hana sha da fataucin wiwi suka kama ta.
An kama dan sandan da ke rakiyar motar tare da direban da kuma wasu ‘yan sandan biyu da ake harkallar tare da su.

Share.

game da Author