A yi koyi da karantarwar Annabi (SAW) – Shehu Abdulkarim Zariya

0

Shehu Sani Khalifa Abdulkadir Zariya, Mataimakin Shugaban Kungiyan Fityanul Islam na Kasa, ya ce: duk mutumin da ya halarto taron Maulidi, ya dauka ya zo makaranta ne, don ya dauki darasi, idan muka taru a wajen maulidi muna gaya ma mutane cewa Annabi mai hakuri ne da gaskiy da amana da alkawari, bawai muna bada labarin kyawawan dabi’un Annabi kawai bane, a’a muna fada ma mutane ne don su yi koyi da shi. Annabi salla lahu alaihi wasallam ya tara halayyan kirki gaba daya, ba sai ka kwaikwayi halayen duka ba domin baza ka iya ba, amma idan kayi kokari ka riki koda hali daya daga cikin halayen Annabi salla lahu alaihi wasallam ya isheka arziki duniya da lahira. Idan ka zamo mai hakuri, labarin kirkinka zai cika garinku, idan ka zamo mai gaskiya, labarin kirkinka zai cika garinku, kazalika idan ka zamo mai kyauta labarin kirkinka zai cika garinku.

Idan ka zama mutumin kirki mutane suka shaida kai mutumin kirki ne, ka samu shahadar shiga Aljanna, hakazalika idan ka zama mutumin banza mutane suka shaida kai mutumin banza ne, ka samu shahadar shiga Wuta, kamar yanda ya zo a hadisi cewa wata rana an wuce da janaza ta gaban Annabi salla lahu alaihi wasallam, sai mutane suka yi kirari na alhairi ga mamacin, sai Annabi ya ce, ta wajaba, sannan daga bisani aka kara wucewa da wata janazan sai mutane suka yi kirari na sharri ga mamacin, sai Annabi ya ce ta wajaba, sai sayyiduna Umar ibnul hadab (R.A) ya ce, menene ta wajaba ? Sai Annabi salla lahu alaihi wasallam yace: wancan da kuka yabeshi da cewa mutumin kirki ne Aljanna ta wajaba a gareshi wannan kuma da kuka shaideshi da cewa shi mutumin banza ne wuta ta wajaba a kanshi, domin kune shaidun Allah a doron kasa.

Shehin malamin yayi wannan jawabin ne a wajen taron gangamin maulidin da ya gudana a garin Zaria a Kofar fadan mai martaba Sarkin Zazzau.

Share.

game da Author