TAMBAYA: Menene hukuncin shan maganin Tari (Codein) da tabar Shisha da ya zama ruwan dare a musulunci ?

0

TAMBAYA: Menene hukuncin shan maganin Tari (Codein) da tabar Shisha da ya zama ruwan dare a musulunci ?

AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.

Babu shakka ta’amuli da kayan maye da tabar shisha ko dukkan wani kayan shaye-shaye haramun ne a musulunce, domin tsananin cutarwan su da tuzarta dukiya. Kwararrun likitoci na jiya da yau sun tabbatar da cutarwan shisha da maganin tari. Allah Ta’ala ya haramta ma dan Adam mu’amala da dukkan abinda zai cutar da jikin sa, hankalin sa, mutuncin sa da dukiyar sa.

Wajibi ne ga dukkannin mai ta’amuli da kayan maye ya barsu kuma yaji tsoron Allah akan haka.

Dukkan malamai sunyi ittifaki akan haramcin kayan maye da tabar shisha, wannan haramci ya kunshi sarrafa su, kasuwancin su, shuka su, dakon su, da dukkanin wata mu’amala da su.

Allah ta’ala yace “ suna tambayanka me aka halatta musu, ka ce an halatta muku dukkan abu mai kyau” (Suratul Ma’ida 4) kuma Allah yace “ Allah yana halatta musu kyawawan abinci ko abin sha, kuma yana haramta musu munann abubuwa” (Suratul A’arafi 157).

Ya Allah katsaremana imaninmu da mutuncinmu. Amin.

Share.

game da Author