Shugaba Muhammdu Buhari ya umarci a gaggauta maida wa Gwamnan Jihar Anambra jami’an tsaron sa da aka sauya.
Yayin da ya key i wa Shugaban Kasa lale marhabin da zuwa Awka domin Babban Taron APC gwamnan ya yi wa Buhari korafin cewa Sufeton ’Yan Sanda na Kasa musanya masa jami’an tsaro.
An dai cire jami’an tsaron ne a ranar Talata, inda aka yi zargin shugaban ’yan sanda na kasa ne da kan sa ya bada umarnin a sauya su.
Kafin Buhari ya bar Awka, Ya umarci Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda Joshak Habila, da ya tabbatar da maida wa gwamnan jami’an tsaron sa.
Dama kuma PREIUM TIMES ta ruwaito cewa Majalisar Dattawa ta yi tir da sauya jami’an tsaron gwamnan a daidai gabatowar zaben jihar sa, inda ya ke neman yin tazarce.
Gwamna Obiano na neman yin tazarce ne, a karkashin jam’iyyar APGA. ’Yan takara 36 ne za su fafata da shi a ranar Asabar mai zuwa, ciki har da Tony Nwoye na jam’iyyar APC.