Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan, ya maida martanin zargin da tsohuwar shugabar EFCC, Farida ta yi masa cewa shi ne ya daure gindin yadda aka rika wawurar kudade a lokacin mulkin sa.
Jaridar Punch ta ranar Lahadi da ta gabata, ta ruwaito Farida na ikirarin cewa Jonathan ya kore ta daga aikin EFCC ne saboda ta ki yarda ta daina binciken daya daga cikin tantiran da suka yi harkallar kudin tattafin man fetur.
Jaridar ta ci gaba da ruwaito Waziri na cewa ta yi hamdala da Jonathan ya cire ta, domin ba wanda zai rika danganta ta da gwamnatin harkalla, gwamnatin Jonathan.
“Ina farin cikin cewa dukkan tabargazar da aka yi lokacin Jonathan, ba na kan aiki na ne.
“Kuma dalili kenan ya sa ko a yau zan ga Jonathan, zan tsuguna na gode masa saboda martaba ni da ya yi ya cire ni daga EFCC, a lokacin.”
Sai dai kuma wadannan kalamai ba su yi wa Jonathan dadi ba, domin ya shiga shafin sa na Twitter a yau Laraba ya caccaki Farida Waziri.
“Idan Farida ba karya ta ke fada ba, ai sai ta fito ta bayyana sunan mutumi ko kamfanin da ta ce na hana ta bincika.”
Jonathan ya kara cewa kawai dai an dauko Farida a matsayin sojar-haya ce, domin ta ci masa zarafi.
Jonathan dai na ci gaba da shan caccaka tun bayan da ya sha kaye a zaben 2015, inda ake dora masa laifin bari aka rika wawurar kudaden Najeriya.
Shi kuma tun ya na kan mulki ya ke kare gwamnatin sa, tare da cewa masu sukar gwamnatin ba su kallon alherin da ya shuka, sai matsalolin ta.