Antibiotics magani ne dake warkar da cutar da ke da dauke da kwayan cuta da ake kira ‘Bacteria’.
Masana da likitoci sun koka kan yadda mutane ke amfani da irin wadan nan magunguna, wasu da yawa ba tare da umarnin likita ba wanda hakan ya sa sun dai na yin aiki a jikkunan mutan.
Kungiyar kula da kiwon lafiyar ta duniya WHO ta ce sakamakon haka ana fama da karancin magungunan sannan wanda ke da karfin yin aiki a jikin mara lafiya cikin su na da dan karan tsada.
Abin da ya kamata ka sani game da irin wadannan magunguna sun hada da:
1. A nemi izinin likita kafin a fara amfani da irin wadannan magunguna.
2. ‘Antibiotics’ ba ya maganin cutar da ke dauke da kwayar ‘Virus’ kamar tari, mura da sauran su.
3. A yawaita yin tsafta a inda ake domin shine babban kariya ga lafiyar ka.
4. A tabbata ana amfani da maganin ne kan cutar da ya kamata.
5. Ayi kokari a sha su zuwa iya yadda aka rubuta wa mara lafiya
6. A dai na ba dabbobi