‘Yan Najeriya suna amfani da kororo roba Miliyan 400 duk shekara

0

Wata kungiya mai zaman kanta ‘Society For Family Health’ ta ce bincike ya nuna cewa sama da kororo roba miliyan 400 ne ake amfani da su a Najeriya duk shekara.

Shugaban kungiyar Bright Ekweremadu ya sanar da haka a taron wayar da kan mutane mahimmanci amfani da kororro roba da ka yi a jihar Legas .

Ya ce bincike ya nuna cewa mafi yawa daga cikin mutane basu amince da yin amfani da kwarorro roba duk da irin wadannan yawa da aka samu.

Ya kara da cewa yin amfani da shi kan samar da kariya ga kamuwa daga cututtukan da ake kamawa wajen juma’i da hana cikin da ba’a shirya masa ba.

Share.

game da Author