Buhari ya bayyana dalilin tsaikon nada mambobin gudanarwar hukumomi

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana dalilan da su ka kawo masa tsaikon nada mambobin gudanarwar hukumomin gwamnati.

Da ya ke jawabi a yayin taron Shugabannnin Kwamitin Koli na jam’iyyar APC, dangane da abubuwan da ke faruwa a cikin jam’iyyar.

Rashin nada wadannan mambobin gudanarwar hukumomi da ya kawo tsaiko sosai wurin gudanar da ayyuka a ma’aikatu da hukumomin na gwamnatin tarayya.

PREMIUM TIMES a baya ta ruwaito wani rahoto inda Shugaban Kungiyar Likitoci ta Kasa, Mike Ogirima, ya dora alhakin yawaitar likitocin bogi a kan rashin kafa mambobin gudanarwar hukumar MDCN, mai sa ido a kan likitoci da al’amurran lafiyar al’umma.

Sai dai kuma a yayin da ya ke jawabi, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana wasu dalilai kamar haka:

“A shekarar da ta gabata na shaida muku cewa zan sake nada Mambobin Hukumomin Gwamnati. Ina matukar ba ku hakurin rashin samun damar yin haka, sakamakon wasu dalilai.

“Wasu daga cikin mahalarta taron nan na sane da cewa an umarce ni tun a cikin 2015 da na yi wannan aikin sabbin nade-naden, to amma sai muka fuskanci tsaiko daga wasu kwamitoci masu yawa, domin a tabbatar an samu daidaito wajen yin nade-naden da nufin a tabbatar kowane yanki na kasar nan ya zamu wakilci daidai yadda ya dace.

“A daya bangare kuma, ina sane da cewa magoya bayan mu sun kagara su ga an yi wadannan nade-naden. Da yardar Allah za mu yi hakan nan ba da dadewa wa. Musamman ma ga shi a yanzu tattalin arziki na samun inganci, za mu samu halin kulawa da dukkan wadanda za a nada a dukkan hukumomin.

“Haka nan kuma za a kara yawan ministoci domin a kara yawan hannayen daukar jinkar Gwamnatin Tarayya, ta yadda za a kara samun masu sabbin hikimomi da fasahar inganta al’amurran gwamnati.”

Share.

game da Author