Sanata na so a rage alawus din ‘yan siyasa

0

Sanata mai wakiltar Osun ta Tsakiya, Olusola Adeyeye, ya yi kira da aka zaftare alawus-alawus da ake ba dukkan zababbun shugabanni a kasar nan, har da sanatoci.

Wannan kalami na Adeyeye ya jefa Majalisar Dattawa cikin rudu da hatsaniya, yayin da ake tafka mahawarar kasafin kudi na 2018.

Adeyeye ya ce tulin kudaden da ake ba zababbun masu mukaman siyasa ciki har da Sanatoci, ya yi yawan gaske, tilas a rage domin a kara wa kasafin shekara-shekara kudaden shiga.

Ya na kai daidai kan wannan bayani sai mambobin majalisar dattawa su ka yi masa caaa, “sai dai a fara zaftare na ka alawus din.”

“Ai ban ce don an rage ba za mu ji jiki ba, za mu ji jiki, amma kuma kasa za ta amfana. To na ji, kuma na amince, a fara da ni din.” Raddin da Sanata Adeyeye ya maida wa sauran mambobin majalisar dattawa kenan.

“A kowane mako a majalisar nan fa mu na kirkiro wadansu bukatu masu bukatar a kashe kudade, a lokacin da mun fi kowa sanin cewa kudaden shigar kasar nan ba su karuwa.

“Wannan kasafin kudin na 2018 da mu ke tattaunawa, kowa a nan na tambaya da tunanin shin daga ina kudaden za su fito?

“Kowa a nan ya san gaskiya, idan za a fuskance ta, to mu fuskance ta gaba dayanmu.” Inji Sanata Adeyeye.

Share.

game da Author