Sama da mutane 3,000 suka mutu a Tekun Mideterranian

0

Wata kungiyar sa ido kan ‘yan gudun hijira ta kasa da kasa, ta bayyana cewa sama da rayukan mutane 3000 suka salwanta a cikin tekun Miditerranean a cikin shekaru hudu.

Kungiyar ta ce an kiyasta cewa an yi asarar rayuka 3,033 na ‘yan gudun hijira ko kuma masu kaura daga kasashen su zuwa Turai.

Ta ce wannan adadi ya kunshi har daga kasashen Libya da kuma yaron nan dan shekara 10 da aka tsinci gawar sa a gefen tsaunin tekun Girka da kuma wadanda suka mutu a hanyar su ta zuwa Spain.

Kakakin kungiyar, Joel Millman, ya kara da cewa tsallaka tekun Mediterranian na daya daga cikin hijira mafi muni da hadari a duniya.

Daga nan sai ya kara da cewa a cikin 2016, akalla mutane 5,413 ne suka mutu ko suka bata a cikin teku a dunya, a kan hanyar su ta gudun hijira.

Millaman ya kara da cewa ya zuwa ranar Lahadi akwai masu gudun hijira 163,976 da ke cikin Turai wadanda suka shiga nahiyar ta gabar ruwan kasar Italiya.

Share.

game da Author