Ministan Babban Birnin Tarayya, Abuja, Bello Muhammed, ya bayyana cewa za a bullo da tsarin da za a rika karbar haraji ga mazauna Abuja domin a rika gudanar da ayyukan ci gaban babban birnin.
Ya ce maganar gaskiya ita ce gwamnatin tarayya ba ta iya daukar nauyin gudanar da komai ko gina kowane titi a Abuja. Ya ce idan mazauna birnin na so a ci gaba da ayyukan more rayuwa a Abuja, to sai an rika karbar harajin da za a yi ayyukan daga aljifan su.
Bello ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya ke duba wani titi da kamfanin gine-gine na Gilmort Engineering Ltd, suke kan ginawa a Abuja.
Da bakin sa, ministan ya ce, a da can za a iya samar da ko me ake son samarwa a Abuja. Amma a yanzu gina gida daya tal ma babban tashin hankalin da sai an kashe makudan kudade ne.
“Ina ganin fa ba mu da wani zabi sai dai mu fara tatsar kudaden daga kowane fuloti. Amma babu makawa sai mun kai ga haka.”
“Idan ka kalli yadda fulotai ke tsada a Abuja, sannan ka kalli abin da ake biyan gwamnati idan za a mallaki fili, kudaden da ake biyan gwamnati ba su taka kara sun karya ba.”